Nigeria Early Grade Reading Assessment: Student Response Form (Hausa)

General Instructions
Ina kwana? Sunana _______ kuma ina zaune a _____. Bari in fara da faxa miki/maka ko ni wace ce/wane ne [misali, iyali, firamaren da aka yi, wasanni, da ire-iren haka]. Toh, yanzu ke/kai kuma ki/ka ba ni naki/naka labarin in ji, ko?

Verbal Consent: Read the text in the box clearly to the child.
  • Bari in faxa maki/maka dalilin da ya sa na zo nan a yau. Ni ina aiki ne tare da Ma’aikatar Ilimi, kuma muna son mu ga yadda yara suke koyon karatu. Taimakonki/ka muke so game da wannan aikin.
  • An zavo sunanki/ka ne domin yin wannan gwajin karatu.
  • Ta hanyar amfani da wannan kwamfuta, zan ga lokacin da zai dauke ki/ka karantawa.
  • Wannan ba jarrabawa ba ce, kuma ba wanda zai fadi in an yi.
  • Haka ma, zan yi miki/ maka wasu ’yan tambayoyi game da makarantarku, da kuma gidanku.
  • Ba zan rubuta suna ba, don haka ba wanda zai san cewa amsoshinki/ka ne.
  • Idan kuma muka fara, kika/ka ji ba ki/ka son amsa wata tambaya, shi ma wannan ba komai, sai mu wuce ta.
  • Akwai tambaya? Kin/ka fahimta, mu fara?